- 🚩Ga sakona zuwa ga buhari
◾Farko da gaisuwa bisa tsari
◾Gareka shugaba mai khairi
◾Gwarzon jarumi mai hakuri
◾Dattijo mai abin alfahari
◾Ga godiyarmu gareka nakowa.
◾Baba gareka zanyi sanarwa
◾Zan zayyano hasashe nawa
◾Zan furta damuwar talakawa
◾Don naga wasu suna boyewa
◾In an fada don kai gyarawa
◾Wai sai suce kai ake aibantawa.
◾Munga chanji a fannin tsaro
◾A baya lallai an mana horo
◾Ayanzu kuma an kore tsagero
◾Munbar gudu balle muji tsoro
◾Da zan iya dana shirya taro
◾Don nuna murna harda yabawa.
◾A bangare kayan masarufi
◾Duk kasuwanni sun dau zafi
◾Babu kudi abinda nake nufi
◾Komai yai tsada babu ludufi
◾Wadansu na daura maka laifi
◾Muna Bukatar gyaran gaggawa.
◾Amma talaka yashiga hali
◾Kowa kagansa wulli-wulli
◾Lallai talauci yayi mana kulli
◾Inka gani yazarce misali
◾Ba batun shan lemon kwali
◾Halin yunwa harda kishin ruwa.
◾Baba matasa bamuda aiki
◾Baba wakilanmu basa aiki
◾Kwarai ana yakar cin hanci
◾Anata kama masu zalinci
◾Dukkan barawo baya bacci
◾Allah yasakawa takalawa.
◾Baba talakawa na sonka
◾Tun dadadewa suke zabarka
◾Sun dora duk burinsu akanka
◾Yau ankusa shekara a mulkinka
◾Wuya sukesha ayanzu haka
◾Kunyarka tahana sui furtawa.
◾Baba muna sonka
◾Mungoyi a bayanka
◾In munga kuskurenka
◾Zamu sanar maka
◾Don gyara aikinka
◾Sonka bazaisamu makancewa