About me

Responsive Ads Here

Monday 4 July 2016

Dawowar Shugaba Buhari Daga London

Wakar Dawowar Buhari
Daga
Nazeer M Saulawa
Barka da dawowa baba
Sannun da hanya baba
Ya bayan rabuwa baba
Fatan anyi nasara baba.
Munata kewarka baba
Ciwonka namu ne baba
Damuwa bata kauce ba
Idanuwa basu rintsa ba.
Hutu kajeyi can baba
Ashe ashe baka huta ba
Yawan tunaninnan baba
Da kuma kishin kasa baba
Bazasu barka ka rintsa ba.
Baba mazan fama baba
Yau ka karyata 'yan gaba
Lallai Ta Allah batasu ba
Zaginsu ba komai ne ba.
Makiya da suke gumba
Tsafinsu bai tasiri ba
Zarginsu bazai illa ba
Basu keda mutuwa ba.
Dukkan tsananin gaba
Bazai kare kwanan ba
In lokaci yazo baba
Basai sun nema ba.
Muma masoyanka baba
Zuwanta bazamu sani ba
Tsareta bazamu iya ba
Bata bar kan kowa ba.
Mu hakuri bamu daina ba
Addua bamu daina ba
Zaginka ba alkhairi ba
Bai wuce sa'bon Allah ba.
A kullum munata duba
Fatanmu jindadi baba
Tunda dai mun hau turba
Bamu cire tsammani ba.
Roko nake sarki rabba
Allah yakareka baba
Ya karama lafiya baba
Ya fidda kai kunya baba.
BARKA DA DAWOWA BABA