About me

Responsive Ads Here

Friday, 12 February 2016

▶ILIMI HASKE


Mu Nemi Ilimi, Marar Ilimi Makaho Ne.

⚫Allahu wahidun sarki kaine makurar ilimi
⚫Allahu al-alimu gwani siffarka ce ilimi
⚫Allahu kai kacewa annabi tashi kai ilimi
⚫Allah kalmar dakayi ta farko a qur'ani ilimi
⚫Ya Rabbi nai shirin karambani akan ilimi
⚫Allah ka qaddara in ida bada gadara ba.

⚫Ayanzu zamani na gasar masu  fasaha ne
⚫Ayanzu zamanin matasa masu basira ne
⚫Don naga duniya na fahari da karatu ne
⚫Amma anan kasarmu neman ilimi fa jidali ne
⚫Mai yi na shan wuya bare wanda ke a gida zaune
⚫Akwai barazana garemu idan bamu gyara ba.

⚫Na yarda ilimi shine ke haifarda tunani
⚫A baya na fada abokai sai suka musa ni
⚫Wurinda babu ilimi acikin akwai muni
⚫Kamar aje wuka kayinta a bude kahau tsini
⚫Wallahi jahili kwakwalwa tasa akwai rauni
⚫A wannnan lokaci jahilci ba uzuri ne ba.

⚫Na yarda jahili komai dukiyarsa faqiri ne
⚫Ko kunqi ku fada watarana za yaji kunya ne
⚫Mai kudi jahili abin a fadeshi a nuna ne
⚫Sarki jahili acikin fadarsa fa sauna ne
⚫Dattijo jahili cikin 'ya'yansa fa yaro ne
⚫Koda cikin gidansa bazai lemancin sallah ba.

⚫Zama da jahili baiwuce zama da makaho ba
⚫Bazaiyi tafiya nesa babu dan jagora ba
⚫An samu 'yancin kai amma shi baibar bauta ba
⚫Baisan yayi kuskure ba in ba'a masa bulala ba
⚫Ko mace jahila bazanyi mata farashi ba
⚫Aure da jahila ka lura akwai hatsari baba.

⚫Tayaya zaka bautawa Allah bada karatu ba
⚫Tauhidi da tsarki  ko sallah baka fahimta ba
⚫Hakkin iyaye ko hakkin aure baka gane ba
⚫Balle irinsu zakka ko azumi aiki babba
⚫Sarrafa rayuwa a cikin ilimi shine riba
⚫Mu gane in da rai ayau wataran ba mune ba.

⚫Wayyo yankin Arewa kasar iyaye da dangina
⚫Munada ilimi tun can farkon  tarihina
⚫Munada jarumai kamar gwarzona sardauna
⚫Amma har yau muna bara kan titi dangina
⚫Ina ta wahla talaucin yaki yabar bi na
⚫Mu nemi ilimi ba muyita zaman 'yan baro ba.

⚫Harka ta kimiyya saida ilimi a fahimta ta
⚫Harka ta shari'a ilimi shine ke tsara ta
⚫Tattalin arziki sai mai ilimi ke gane ta
⚫Harkar 'yan jarida kan ilimi aka dora ta
⚫Harkar kasuwanci mai ilimi yaci ribar ta
⚫Hanyoyin ilimi baki bazai yiwu ya kirga ba.

⚫Mai ilimi shine sarki acikin zamaninsa
⚫Mai ilimi yasan ta ya zai sarrafa harshensa
⚫Aiki in yayi kyau duba ilimi ne tushensa
⚫Da ilimi mutum yake iya cimma muradinsa
⚫Babu mutum dake fahar da cikar jahilcinsa

⚫Mu taimakawa mata sui ilimi don gyarawa
⚫Mu fara fadakarwa ko a kafafen sadarwa
⚫Munada nakasassu masu bukatar dubawa
⚫Mu daina nuna ban-banci al'ummar Arewa
⚫Shugabanni ina kira a gareku ku amsawa
⚫Gyaran kayanka bazai zama sauke mu raba ba.

⚫Mu farga 'yan uwa taimakon juna ne wayewa
⚫Matasa mu tashi mu himmatu kar mui zaunawa
⚫Masu kudi ku taimaki 'ya'yan talakawa
⚫Ku kuma malamai ku kara fahimtar koyarwa
⚫Mu shirya tafiya zuwa kauye don wayarwa
⚫Allah ka daukaka Arewa da nigeria babba.

⏩Mu Nemi Ilimi Rashin Ilimi Asara Ne.

28-01-2016